MASIGNASUKAv102
6510051498749449419

Ko kunsan abunda ke sanya Jaruma Hadiza Gabon farin ciki

Ko kunsan abunda ke sanya Jaruma Hadiza Gabon farin ciki
Add Comments
Friday, March 5, 2021


 Hadiza Gabon fitacciyar Jarumar kannywood ta bayya cewa babu abunda ke sata farin ciki kamar taimakawa mabukaci.

Jaruma Gabon ta bayyana hakan ne a wata hira da tayi da jaridar Dailytrust.


Ta bayyana cewa ta yaya mutum zai ji a ranshi cewa yana da kwanciyar hankali don kawai don shi yana da shi, alhalin akwai mabukata dake kwana basu ci abinci ba.


“Yana dakyau mutane su fahimci cewa dan abinda kake ganin ka yi na taimakawa da kyautata rayuwar wasu shine abinda ako da yaushe mutane zasu riƙa tuna ka da shi.”



Hadiza Aliyu Gabon

“Ya na dakyau ako da yaushe mu riƙa ƙoƙarin ganin mun tallafi rayuwar mabuƙatan dake cikin mu.”



 

A ƙoƙarin ganin ta taimaki mabuƙata, jarumar ta ƙirƙiro wata gidauniya a shekarar 2016. Hadiza Aliyu Gabon (HAG) Foundation, gidauniya ce ta jarumar dake ƙoƙarin tallafa ma mutane musamman ta ɓangaren da ya shafi lafiya. Haka nan ma gidauniyar tana kula da abinda ya shafi ilmi da kuma tallafin kayan abinci.


 


Jarumar ta kirayi al’umma da su kasance masu nuna so da ƙaunar juna gami da nuna kulawa wanda idan akai hakan za’a rinka samun saukin matsalolin da ake fuskanta a cikin al’umma.


“Za’a rinƙa samun daidaito da cigaba in ya kasance akwai ƙauna gami taimakon juna a tsakankanin al’umma.”

Shuraih 99%

Talented Aurthor, blogger in fashion and YouTuber in habits, I am living in keffin Magaji Dan Yamusa, Nasarawa state Nigeria, I am specialist at any kind of webdesign,webdevelopment, graphics designer and video editing I can make inpossible to possible with my laptop